WANENE KE SHARI’ANTAWA WANI? 3

A cikin aya ta goma sha biyu, Yakubu ya tunatar da mu cewa, “Saboda haka, maganarku da aikinku su kasance irin na mutunen da za a yi wa shari’a bisa ga ka’idar ‘yanci.” A nan, Yakubu ya gabatar da ma’anar ma’auni na ciki.