WANENE KE SHARI’ANTAWA WANI? 2

Ka tuna da mahallin wannan sashen da muke gani. Kafin ayoyin nassinmu na yau, Yaƙub ya koya mana cewa da akwai muguntar nuna son bambanci ko son zuciya. Ya gaya mana sarai cewa idan muka nuna son kai, mun keta dokar Allah ke nan, kuma muna da laifi a matsayin masu karyar da dokar.