WANENE KE SHARI’ANTAWA WANI? 1

A yau muna ci gaba da nazarinmu a cikin littafin Yakubu. Sakon namu da ya gabata, daga sura ta biyu, aya ta daya zuwa tara mai taken, “Kawar da Nuna Bambanci.” A yau za mu ci gaba a sura ta biyu ta hanyar duba ayoyi da dama na gaba; aya ta goma zuwa sha uku. Kuma wannan binciken namu mai taken, "Wanene ke Shari’anta Wani?”