KAWAR DA NUNA BAMBANCI 3

NA BIYU: ZABE IRIN NA ALLAH Mu ci gaba yanzu zuwa aya ta biyar zuwa bakwai. Mu tuna, cewa a cikin mulkin Allah akwai tsari dabam da na mulkokin ’yan Adam. A cikin mulkin Allah, hanyar da za a ɗaukaka, ita ce kaskantar da kanka. Hanyar zama babba ita ce ka zama bawa.