MADUBI, MADUBIN MAGANAR ALLAH 1

A wata rana a lokacin da ake zubar da dusar kankara kamar yadda gashin kaza yake fadowa daga sama, sai wata kyakkyawar sarauniya tana zaune a bakin tagar ta, wadda tagar an yi da wani bakin katako na itacen eboyi.