Muhimman Zantuttuka Don Rayuwan Krista
-
Zango Na 1: Wane ne Yesu?
Jerin darusan na gabatar da kai ga aikin Yesu daga ra’ayin Kristanci, ta wajen la’akari da Kammaninsa, aikinsa, koyarwarsa, da kuma mutuwarsa. Saboda Yesu na da muhimmanci kuma shi ne cibiyar addinin da kuma koyarwar Bangaskiyar Krista, yakamata almajirin ya san da cewar ya san da Yesu, da kuma waᶑanda ke neman sani a Kristanci su kuma san abin da ya bambanta Yesu Kristi ya kuma zama dabam, ya kuma isa almajiracinmu da kuma yabonmu. Za ka iya samun mahallartan da ke da fahimta dabam-dabam, da al’adu da kuma addinai dabam-dabam game da ko wa Yesu yake da kuma abin da ya koyar. Waᶑannan bayanan da aka jeranta za su iya kasancewa tushe nagari don nazarinsu na nan gaba cikin almajiranci. -
Zango Na 2: Fahimtar Ceto
Waᶑannan darusan na da matuƙar muhimmanci ga kowanne mai ba da gaskiya don ya fahimta kafin su yi yunƙurin kai shelar bishara da inganci ga wasu. Kowanne darasi na binciko wata ra’i ne ko tunani daga abin da Littafi Mai Tsarki ya yi matsaya akai, kuma na kunshe da zarafi don tattaunawa daga ta cikin irin waᶑannan ra’ayoyin ko ka’idodin da kuma yadda za a yi amfani da su a rayukanmu. Wannan zangon na da muhimmanci sosai wajen almajirantar da sabin tuba don tabbatar da cewar sun sami cikakkiyar fahimtar waᶑannan tunanin. -
Zango Na 3: Rayuwar Krista Kwatanta Da Wasu Ra’ayoyin
Darusan da aka jeranta na nazari ne game da ire-iren zaϸuϸϸukan da kuma aikace-aikacen da suke da muhimmanci don rayuwar Krista. A yi rayuwa kamar yadda Kalmar Allah ya koyar mana na nufin mun fahimci da cewar zaϸuϸϸukan da muke yi yau da kullum na da tasiri bisa bangaskiyarmu. Hakan ma na nufin da cewar koyon yadda ake addu’a, yin aiki da dokokin Allah da kuma yunkurin koyon yadda za ka taimaka wa gami da bauta wa wasu. Waᶑannan darusan na da muhimmanci sosai don samun fahimtar yadda ake Kristanci. Haᶑa har da lokaci don tattauna waᶑannan ka’idojin da kuma yadda za mu yi amfani da su a rayuwarmu. -
Zango Na 4: Dangantakarmu Da Allah
Wannan jerin darusan na nazarin dangantakan da muke da shi da Allah. Yakan fara da fahimtar matsayinmu cikin Kristi wanda shi ne sanadin zamanmu ‘ya’yan Allah. Jerin darusan na duban halayen Allah, da yadda ya kamata mu san Shi sosai, da kuma yadda za mu gina wannan dangantakan na kud-da-kud da shi. Fahimtar kanmu ta idanun Allah, da kuma samun kyakkyawan hoton yadda Allah yake, zai taimaka mana mu yi rayuwan da Allah ya tsara mana. -
Zango Na 5: Gabatar Da Shelan Bishara
Wannan jerin darusan na da niyyar shirya mahallartan domin su iya kai shelar bishara da inganci ga wasu . fahimtar yadda Allah yake shirya mu domin hidima da kuma yadda za mu shirya saƙonmu na bishara da za su iya tinƙarar ra’ayoyi dabam-dabam zai taimaka wajen aike wannan saƙon mara canjawa na bege da ake samu cikin Yesu Kristi ga duniyan nan da ba ta san Shi ba har yanzu. -
Zango Na 6: Shelan Bishara Ta Wutirn Amfani Da Ka’idojin Ruhaniya
Wannan dabaran na amfani da ka’idoji na ruhaniya da shugaban Campus Crusade for Christ Bill Bright ya wallafa. Wannan dabaran za a iya amfani da shi wajen tsara shelan Bisharnmu, sannan kuma yana nan a ᶑan littafi don amfani da shi a matsayin kayan aikin shelan Bishara. An kuma buga shi a harsuna da dama ana samunsu a Yanan Gizo, na www.4laws.com. Darusan suna bayani game da ka’idoji ruhaniya huᶑu da kuma yadda za a yi amfani da su ta wurin magana don bayani sannan a gyayyaci jama’a su ƙarϸi Yesu A matsayin mai cetonsu. Lokacin tattaunawa na ƙarfafa amfani da ka’idojin da aka shimfiᶑa. -
Zango Na 7: Almajiranci Na Krista
Darusan na gabatar da horaswan ko tarbiyyan da ke tattare ko da rayuwan Krista, haᶑa har da addu’a, Nazarin Littafi Mai Tsarki, da kuma sanya tunaninmu ga abubuwa na har abadin abada. Hakan batu ne da zai sanya zumuᶑi da zai ƙarfafamu ya kuma janyo sabin Krista ga rayuwar bangaskiya mai zurfin gaske. Kayayyakin aikin nan dai a bayyane suke don a yi amfani da su, duk da hakan ya fi maida hankali ga irin ladan da za ‘a samu a ruhaniyance na rayuwar da a sadauƙar ga Allah. -
Zango Na 8: Allah Da Kuma Duniyar Ruhaniya
Module 8: God and the Spiritual Realm This series of lessons examines the reality of the spiritual world – one in which there are forces of both good and evil. This module deals with the origin of evil, the end punishment of Satan, the reality of spiritual warfare and strongholds in our everyday lives, the armor that God has provided us with, God’s great battle plan against Satan, God’s ultimate control over all things and the supernatural ways in which God occasionally communicates with his people through dreams, visions and angelic beings. Zango Na 8: Allah Da Kuma Duniyar Ruhaniya Jerin darusan na nazarin ne game da duniyar ruhaniya—wanda akwai ikoki na nagarata da na mugunta. Wannan zangon zai fi maida hankali ne ga asalin mugunta , ƙarshen hukuncin da za a yi wa Shaitan, gaskiyar cewar akwai yaƙin ruhaniya da shingayen duhu a rayuwarmu na yau da kullum, makama yaƙin da Allah ya tanada mana gaba da shaitan, shirin babban yaƙi na Allah da gaba da Shaitan, yadda Allah ke da mulki bisa komai da komai da kuma hanyoyin masu girma na ikon Allah da ya tanada da sau da dama yakan yi magana da mutanen ta wurin mafarki, wahayai da ziyarar mala’iku.
Muhimman Zantuttuka Don Shugabancin Ruhaniya
-
Zango Na 1: Binciko Matakan Almajiranci
Jerin darusan na nazari ne dangane a matakan gina ruhanuniyar masu bin Yesu Krsiti—abin da ake nufi da almajiranci. Matakan almajirancin kan samu ne bayan mutum ya zo ga sanin Yesu Kristi ta wurin bangaskiya, fara daga muradin tafiyar da shirin Allah don rayuwarmu. Yayin da muka ᶑau matakin taimakawa sabon tuba don ya girma cikin bangaskiya, anan ana nufin muna masa almajirantaswa ne. Wannan kayan aikin zai taimaka maka yayin da kake marmarin ka almajirantar da wasu, musamman ma waᶑanda suke yin aikin kai shelan Bishara, suna renon sabin tuba suna taimaka musu su girma cikin bangaskiya. Almajirantarwa aiki ne na kowanne mai bi na kwarai, musamman ma waᶑanda ke cikin shugabannin ruhaniya! -
Zango Na 2: Bishe Da Ƙananan Kungiyoyi
Makasudin darasin shi ne a shirya gina rayuwar shugaba da kwarewar ko sani da kuma fahimtar da zai taimaka masa ya zama mai nasara cikin jagoran ƙananan kungiyoyi, Kungiyar zai iya kasancewa ta nazarin Littafi Mai Tsarki ko kungiyar almajiranci, ko wata ƙaramar kungiyar da ake amafani da shi don zumunta da aikin hidima. Abin mai da hankli shi ne dangantaka mai inganci da na kwarai, tafe tare da halin ƙauna da yi wa juna bauta. Shirya kanka don ka kasance shugaba na kwarai a kungiyar yana inganta iyawarka don ka taimaka wa wasu almajiran su ma, a zubi guda kuma, samar da wata damar jin daga kowa da kowa. Wannan zangon an shirya ta ne don waᶑanda a yanzu suke shugabanci, ko memban wata ƙaramar kungiya. Mai yiwuwa membobin ƙananan kungiya wataran za su ᶑauki ragamar shugabancin wannan kungiyar. -
Zango Na 3: Baye-bayen Ruhaniya
Zangon na nazarin fannoni da dama na baye-bayen ruhaniya da aka ambato a cikin Nassi, sannan da yadda mai bi zai iya amfani da waᶑannan baye-bayen ya bauta wa Allah da kuma mutanen. Mahallartan za a basu jagoran yadda za su gano baye-bayensu na ruhaniya su da wasu da ke kewaye da su. Za su sami ƙarfafa sosai da za su sanya baye-bayen nan ga aiki , don cimma manufar Allah, ta wurin bauta wa juna da kuma yin sujada cikin ruhu da gaskiya. -
Zango Na 4: Ikkilisiyan Da Kuma Sujada
Jerin darusan na nazarin abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da manufar ikkilisiya da yadda ta samu ta kasance. Shugabannin Ikkilisiya na bukatan su kasance kafaffu da gindinsu cikin fahimtar abin da ya sa Yesu Kristi ya kafa Ikklisiya da kasancewa a matsayin jiki guda ( Jakadunsa a wannan duniyar) bayan da Ya haura zuwa sama. Ikkilisiya, cike da iko ta wurin Ruhu Mai Tsarki, an umarceta da ci gaba da shelan Bishara a duk kewayen duniya da ta yi bauta a dukannin al’umominta. Tana kuma saduwa akai-akai su yi wa Allah sujada, a gargadar da su cikin maganar Allah, sannan kuma su mara wa juna baya ko su taimaka wa juna. -
Zango Na 5: Rayuwar Iyali
Jerin darusan na duban shugabanci na ruhaniya a gidajenmu kamar dai yadda kunshi gina gidan Krsita mai inganci. Yakan fara ne da tsari na fahimtar abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da makasudin iyalai kansu, irin su shiri don a yi aure, sarrafa kuᶑi a iyali, shugabantan Yara, da kuma gina kafar sadarwa nagari da abokan zama. Wannan jerin darusan na nunawa da cewar shugabanci na Ruhaniya dai daga gida ne ake samunsa tukuna—dukansu mata da maza, na da ayuka ko hakkokin da ya rataya a wuyansu. Darusan na nuna shirin Allah kyakkawa don iyalai, yayin da ya amince da cewar a duniyarmu ta yau iyalai za su iya samuwa ta fuskoki da dama. Darusan za su taimaka wa waᶑanda ke da aure, waᶑanda ke da wata aiki don magidanta, da kuma matasa waᶑanda ke biᶑan dangantaka nagari a nan gaba. -
Zango Na 6: Salon Shugabanci
Darasin dai na nazari ne na fitattun hanyoyin da ake bukata daga waᶑanda ke shugabanci. Zama shugaban fa ya fi a tashi a gaban jama’a ana musu Magana ko ace su biyo mu! In har za ka zama shugaba nagari to dole mutum ya kasance da rayuwa marar abin zargi ko a ϸoye ko kuma a ganin jama’a. Yayin da kowannenmu na gwagwarmaya ta hanyoyi da dama, shugaba dole ne yana fuskantan gwagwarmaya da ƙalubale da dama na musamman. Wannan Zangon zai zakulo wasu daga cikin irin waᶑannan gwagwarmayan da shugaba ke shigewa ciki da kuma yadda zai shawo kansu ya magance su, tare da ba da bayanai kwarara ga mata da mazan da suka fuskanci irin waᶑannan gwaje-gwajen da kuma farincikin da ke tattare da bin kiran Allah a shugabancinmu. Kowanne darasin na ƙarewa da wata shafi na daga shugaba zuwa shugaba. Yana tafe da wasu bayanan da aka ruwaito daga manyan shugabanin Krista da kuma shugabanni na yanzu, da ma sauran mutane ( da basa ma shugabanci ) da suke da abubuwan da suka ᶑanᶑana da za su yi Magana bisa ga wannan kan maganan. -
Zango Na 7: Gina Halin Krista
-
Zango Na 8: Gafara Da Sulhu
-
Zango Na 9: Koyarwan Krista
-
Zango Na 10: ‘Yan Bayanai Don Aikin Pasto
- Wane ne Yesu?
- Fahimtar Ceto
- Rayuwar Krista Kwatanta Da Wasu Ra’ayoyin
- Dangantakarmu Da Allah
- Gabatar Da Shelan Bishara
- Shelan Bishara Ta Wutirn Amfani Da Ka’idojin Ruhaniya
- Almajiranci Na Krista
- Allah Da Kuma Duniyar Ruhaniya
- Binciko Matakan Almajiranci
- Bishe Da Ƙananan Kungiyoyi
- Baye-bayen Ruhaniya
- Ikkilisiyan Da Kuma Sujada
- Rayuwar Iyali
- Salon Shugabanci
- Gina Halin Krista
- Gafara Da Sulhu
- Koyarwan Krista
- ‘Yan Bayanai Don Aikin Pasto