WANENE KE SHARI’ANTAWA WANI? 3

A cikin aya ta goma sha biyu, Yakubu ya tunatar da mu cewa, “Saboda haka, maganarku da aikinku su kasance irin na mutunen da za a yi wa shari’a bisa ga ka’idar ‘yanci.” A nan, Yakubu ya gabatar da ma’anar ma’auni na ciki.

WANENE KE SHARI’ANTAWA WANI? 2

Ka tuna da mahallin wannan sashen da muke gani. Kafin ayoyin nassinmu na yau, Yaƙub ya koya mana cewa da akwai muguntar nuna son bambanci ko son zuciya. Ya gaya mana sarai cewa idan muka nuna son kai, mun keta dokar Allah ke nan, kuma muna da laifi a matsayin masu karyar da dokar.

WANENE KE SHARI’ANTAWA WANI? 1

A yau muna ci gaba da nazarinmu a cikin littafin Yakubu. Sakon namu da ya gabata, daga sura ta biyu, aya ta daya zuwa tara mai taken, “Kawar da Nuna Bambanci.” A yau za mu ci gaba a sura ta biyu ta hanyar duba ayoyi da dama na gaba; aya ta goma zuwa sha uku. Kuma wannan binciken namu mai taken, "Wanene ke Shari’anta Wani?”

KAWAR DA NUNA BAMBANCI 3

NA BIYU: ZABE IRIN NA ALLAH Mu ci gaba yanzu zuwa aya ta biyar zuwa bakwai. Mu tuna, cewa a cikin mulkin Allah akwai tsari dabam da na mulkokin ’yan Adam. A cikin mulkin Allah, hanyar da za a ɗaukaka, ita ce kaskantar da kanka. Hanyar zama babba ita ce ka zama bawa.

KAWAR DA NUNA BAMBANCI 2

NA DAYA: MATSAYI NA RASHIN GASKIYA Don gabatar da wannan batun, ina so in fada muku wata wasiƙa ta tatsuniya. Bari ku saurara ku ji abin da take magana.

KAWAR DA NUNA BAMBANCI 1

A cikin shekarun da suka gabata na kan tafi farautar makwarwa a jeji lokaci zuwa lokaci. Idan kun taba farautar makwarwa a jeji kun iya sanin dabarar farautar kamata.

MADUBI, MADUBIN MAGANAR ALLAH 3

Sabanin hakan an bayyana shi a cikin aya ta ashirin da biyar tare da Kalmar, amma. Duk wanda ya dubi kansa a madubin maganar Allah, sai kawai ya juya, ya tafi abin sa batare da ya yi wani canji a cikin rayuwarsa ba, a banza ne.

MADUBI, MADUBIN MAGANAR ALLAH 2

Yana iya yuwuwa cewa dukan mu mun taba samun kanmu a wani yanayi na taba tafiya a kusa da madubi. Bama tsaya mu dubi yanayin kasancewarmu; mu kan dan de duba abin kadan daga idanunmu.

MADUBI, MADUBIN MAGANAR ALLAH 1

A wata rana a lokacin da ake zubar da dusar kankara kamar yadda gashin kaza yake fadowa daga sama, sai wata kyakkyawar sarauniya tana zaune a bakin tagar ta, wadda tagar an yi da wani bakin katako na itacen eboyi.

CIN NASARA DA GWAJE-GWAJE 3

Wataƙila kuna mamakin inda na ga wannan ƙa'idar ko hanyar. To, a nan ne a karshen aya sha biyar kuma a cikin aya ta goma sha shida. Kamar yadda na ambata a batu na baya, zunubi yana kawo canji a dangantakarmu da Allah. Yanzu kafin ka yanke shawara, ban ce da zarar ka yi zunubi ba ka rasa cetonka.

CIN NASARA DA GWAJE-GWAJE 2

NA DAYA: Mu Karɓi Kasancewar Kalma a Cikin jiki A cikin ayoyin da suka gabata a nassinmu, Yakubu ya ci gaba da bayani akan gwaje-gwaje ko jaraba. Ana shuka iri na ra'ayi a cikin tunani ta wurin sha'awarmu.